Firaministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi watsi da shirin kafa gwamnati, bayan dukkan yunkurinsa na cimma wannan burin ya ci tura.

Hakan dai ya bude wa babban abokin hammayarsa, Benny Gantz, damar neman kafa gwamnatin, domin kawo karshen watanni shida na rikicin siyasar haramtacciyar kasar Isra’ilar.

Wannan dai babban koma baya ne ga firaminsitan haramtacciyar kasar Isra’ilar bayan shafe sama da shekaru goma yana jagorancin gwamnatin.

Sai dai masana ga ganin ko shi Benny Gantz zai iya gaza kafa gwamnatin hadakar, wanda idan hakan ta kasance shugaba Reuven Rivlin, zai bukaci ‘yan majalisa masu rijaye su zabi dan takara.