Shugaban Hukumar kula da shige da fice ta kasa a Nigeria mohammad Babandede shi ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da manema labarai, yana mai bayyana cewa nan ba da jimawa ba za’a sanar da sabon Nau;I 3 na ba da Visa wato izinin shiga kasar, kamar ta masu zuwa yawon bude ido, da kuma ta masu son sanya hannayen jari, da kuma wadanda suka yi ritaya a kasahen wajen amma suna son zama a Nigeria.

Har ila yau ana karfafa guiwa ga wadanda ke da kudi su shigo kasar domin zuba hannayen jari wanda hakan zai taimaka matuka wajen karfafa tattalin arzikin kasar.

Wani jami’i ya shaidawa manema labarai cewa taron shekara- shekara da shugaban hukumar kula da shige da fice na kasar ya shirya a karfafa guiwa wajen yin aiki tare daya sanya a kasa samu cin nasara wajen kawo sabbin sauye –sauye a cikin hukumar a cikin dan kankanin lokaci.

Daga cikin nasarorin da aka samu shi ne daidaita yadda ake samun passport cikin sauri, domin anaso yan Nigeria su san yadda ake samun Passport kana za’a daidaita farashin passport yadda kowa zai iya mallakar sa.

Daga karshe ya nuna cewa duk wani sauyi da za mu kawo muna la’akari da yanayin tsaron kasa domin shi ne akan gaba.