A jamhuriyar Nijar, mutane kimanin 23,000 ne ambaliyar ruwan sama ta raba da muhallensu a jihar Diffa dake kudu maso gabashin kasar.

Ruwan sama da aka samu masu yawan gaske a makwannin baya bayan a yankin, sun sanya kogin Komadugu Yobe, dake kai ruwa a tafkin Chadi, tumbutsewa, kamar yadda ‘yan majalisar dokoki kasar daga jihar ta Diffa suka fitar a majalisar dokokin kasar.

Bayanai da gidan radiyo kasar ya fitar na ‘’voix du Sahel’’ ya fitar sun ce an samu kauyuka biyu da amlaliyar ta lalata, sai kuma gonnakin shinkafa da dama da suma suka lalace.

Wannan lamarin dai ya sanya al’amuran jin kai sun kara tabarbarewaa yankin da ya jima yana fama da matsalar Boko haram.

Dama kafin hakan alkalumman da gwamnatin kasar ta Nijar ta fitar, sun nuna cewa mutane 57 ne suka rasa rayukansu, a ambaliyar ruwan da aka fuskanta a kasar a tsakanin watam Yuni zuwa Satumban da ya gabata.