Gwamnatin Jamhuriya Nijar ta dauki matakin haramta wa kungiyoyin agaji shiga a yankunan dake fama da matsalar tsaro a jihohin Tillaberi da kuma Tawa.

wata sanarwa da ma’aikatar cikin gidan kasar ta fitar, ta ce an dau wannan matakin ne saboda tabarbarewar al;amuran tsaro a yankunan, don haka daga yanzu an haramtawa kungiyoyin agaji shiga wadannan yankunan dake karkashin dokar ta baci, idan ba tare da rakiyar sojoji ba.

A sanarwar da ministan cikin gidan kasar Bazum Mohammed, ya sanya hannu ya bukaci shugabar ofishin kula da ayyukan jin kai a kasar data tabbatar wannan umarnin ya isa kunnen dukkan kungiyoyin agaji na MDD da kuma na kasa da kasa dake a Nijar, sun yi aiki da wannan dokar.

Matakin na gwamnatin Nijar, na zuwa ne a daidai lokacin da ake yawaitar fuskantar kwace-kwace na motocin kungiyoyin agaji da kuma na gwamnatin kasar, a wadannan yankunan dake raba iyaka da kasashen Mali da Burkina Faso, dake fama da matsalar gungun ‘yan ta’adda.