Tsohon Firai ministan kasar Iraqi kuma shugaban gamayyar jam’iyyu ta “Daulatul Qanoon” Nuri Al-Maliki ya yi gargadi wa kawancen sojojin masu yakar yan ta’adda a kasar Iraqi dangane da farfadowar yan ta’adda a kasar a cikin wannan halin da kasar ta ke ciki.

Tashar talabijin ta Al-Alam mai watsa shirye-shiryensa da harshen larabci a nan Tehran ta nakalto Al-Maliki yana fadar haka a yau Laraba, a lokacinda yake tattaunawa da hafsan safsoshin sojojin kawance a kasar ta Iran wanda ya kai masa ziyara a ofishinsa a birnin Bagdaza.

Al-Malika ya kara jaddada muhimmancin aiki tare tsakanin jami’an tsaro na kawancen yaki day an ta’adda a kasar Iran da kuma sauran jami’an tsaron kasar ta Iraqi, musamman dakarun Hashdushaabi, don tabbatar da cewa yan ta’adda basu yi amfani da rigingimun da suka faru a cikin yan kwanakin da suka gabata, don kai farmaki kan mutanen kasar Iraqi.

A ganawar dai bangarorin biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin taro a cikin kasar ta Iraqi da kuma yankin gabas ta tsakiya.