Yawan danyen man fetur da ake fitarwa a kasuwannin duniya ya ragu sosai a cikin watan satumban day a gabata, saboda hare-haren da aka kaiwa kamfanin man fetur na ARAMCO a kasar Saudia a ranar 14 ga watan.

A wani bincike wanda kamfanin dillancin labaran reuters ya gudanar ya gano cewa kasashen kungiya OPEC guda 14 sun haka danyen man fetur ganga miliyon 28.9 a ko wace rana bayan harin, wanda ya samar da gibin ganga 750,000 a ko wace rana, idan an kwatanta da watan Agustan day a gabata.

Rahoton ya kara da cewa takunkuman hana kasashen Iran da Venezuela saida danyen man fetur nasu ya kara kawo tashin farashin man zuwa dalar Amurka 72 kan ko wace ganga.Sai dai wannan farshin ya sake yin kasa bayan da sauran kasashen suka gaggauta cike gibin, wanda ya maida farashin danyen man zuwa dalar 61 a halin yanzu.

A watan decemban shekara da ta gabata ce kasashen kungiyar OPEC da kuma Rasha suka amince da rage yawan man da suke haka a ko wace rana da gangan miliyon 1.2 a ko wace rana.