Fira ministan kasar Indiya Narendara Modi ya bukaci kasar Paskitan da ta bashi damar yin amfani da sararin samaniyar kasarta , domin yin tafiya, sai dai ta yi wasti da bukatar tasa, biyo bayan rikicin dake faruwa a yankin Kashmir.

Duk da yake cewa ba’a bayyana inda Modi zai je ba a cikin bayanin da aka fitar, amma wani babban jami’in gwamnatin kasar Pakistan ya fadi cewa Fira ministan yana son yin tafiya ne zuwa kasar Saudiya.

Wannan dai shi ne karo na 3 acikin mako guda da gwamnatin Islamabad ta hana Jami’an kasar Indiya yin amfani da sararin samaniyarta, tun awatan Febrairu ne Pakistan ta rufe sararin samaniyarta ga kasar Indiya bayan da dakarunta suka kai hari a wani wuri da suke ce sansanin yan ta’adda ne yankin Balakot dake kasar Pakistan.

Ta bayyana harin a matsayin mayar da martani kan harin da aka kai a wani bangaren yankin Kashmir dake karkashin ikon kasar Indiya da ya yi sandiyar kashe sojojinta guda 40.