A wani jawabi da ya yi ta gidan talbijin din kasar, pira ministan Iraqi Adel Abdul Mahdi ya bayyana cewa ya bukaci majalisa ta kada kuri’ar canzawa wasu ministoci ma’aikatunsu, kuma ya lashi takobin mika daruruwan sunayen wadanda ake zargi da hannu wajen rura wutar Zanga-zangar da ta gudana a kasar gaban kuliya manta sabo domin hukumtasu.

Har ila yau ya sanar da kwanaki 3 domin yin zaman makoki a fadin kasar, domin nuna alhini da kisan mutane 110 da aka da kuma jikkata sama da mutum 600, sakamakon taho mu gama da aka yi tsakanin jami’an tsaro da masu Zanga- zangar nuna kin amincewa da kunci rayuwa da matsatsin tattalin arziki da alummar kasar ke ciki, a birnin Bagadaza da wasu yankunan dake kudancin kasar.

Ya ci gaba da cewa: mun umarci jam’ain tsaro da kada su yi amfani da harsashi mai rai kan masu Zanga- zanga, amma duk da haka sai da aka samu rasa rayuka sosai. Tuni dai gwamnati ta sanar da sabon tsarin biyan albashi ga ma’aikatan gwamnati a matsayin matakin farko na amsa bukatun masu Zanga- zangar.