Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya bayyana cewa, abbu wani dalili da ke tabbatar da cewa Iran ce ta kai hari kan kamfanin Aramco.

Tashar presstv ta bayar da rahoton cewa, a lolacin da yake halartar taron karawa juna sani kan makamashi na kasa da kasa da aka bude a birnin Moscowajiya, shugaba Putin ya bayyana cewa, bai amince da zarge-zargen da wasu ke yi kan kasar Iran ba, na cewa ita ce ta kai hari kan kamfanin Aramco, domin kuwa babu wani dalili da ya tabbatar da hakan.

Tun bayan kai harin da mayakan kasar Yemen suka yi kan babban kamfanin main a Saudiyya a ranar 14 ga watan Satumban da ya gabata, Amurka da wasu kasashen turai sun da ita kanta Saudiya sun zargi Iran da kai harin.

Dakarun klasar Yemen da suka hada da dakarun sa kai na kabilun larabawan kasar, sun nuna hotunan yadda suka kai harin, wanda ya lalata babban kamfanin mai na Aramco.

Bayan haka kuma a ranar Asabar ad ta gabata dakarunna Yemen sun kai wani harin a kan wasu barikokin sojin Saudiyya a yankin Najran da ke kudancin Saudiyya, inda suka kame sojoji fiye da dubu 2000 da kuma kashe wasu daruruwa a usayar wutar da suka yi.