Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, dole ne kasashen yankin gabas ta tsakiya su mutunta Iran a matsayinta na daya daga cikin kasashen yankin.

A lokacin da yake zantawa da wasu manyan tashoshin talabijin a jiya a birnin Moscow, shugaba Putin ya bayyana cewa, yana kiran kasashen yankin gabas ta tsakiya musamman kasashen yankin tekun fasha da suke makwabtaka da Iran, da su mutunta kasar ta Iran a matsayin daya daga cikin kasashe makwabta.

Ya ce kasar Iran tana da samuwa a wannan yanki tun dubban shekaru da suka gabata, a kan haka babu wanda zai iya mayar da ita saniya ware a cikin yankin gabas ta tsakiya.

Dangane da hare-haren da Turkiya take kaddamarwa a kan Kurdawa a rewacin Syria kuwa, Putin ya ce dole ne duk wata kasa da ta shiga cikin Syria ba tare da izinin gwamnatin kasar Syria ba, ta fice daga kasar, domin hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa.

Ya ce sojojin gwamnatin kasar Syria ne suke da hakkin kare iyakokin kasarsu, kuam su ne ya kamata su karbi iko da wadannan yankunan da ake rikici a cikinsu.