Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Rabiei: Iran Za Ta Ci Gaba Da Kokari Tabbatar Da SulhuKakakin gwamnatin jamhoriyar musulinci ta Iran ya tabbatar da cewa masu bakar aniya su sani, Iran ba za ta dakatar da kokarin da take yi ba na karfafa sulhu da abotaka tare da kasashen dake makwantaka da ita a yankin.

Yayin da yake gabatar da taron manema labarai a wannan Litinin, kakakin gwamnatin kasar Iran Ali Rabiei ya yi ishara kan irin makircin da makiya ke kullawa na rusa kyakyawar alakar dake tsakanin kasar Iran da kasashen dake makwantaka da ita, inda ya ce kamata yayi kasashen yankin tekun fasha su zamanto masu basira da luka a game da makircin makiya.

Rabiei ya kara da cewa manufar jamjoriyar musulinci ta Iran shi ne karfafa alaka da kuma sulhu a tsakakin kasashen dake makwantaka da ita musaman ma kasashen yankin tekun fasha.

Yayin da ya koma kan kasar Iraki, Rabiei ya nuna damuwarsa kan abinda ya faru a kasar cikin’yan kawankin nan inda ya ce kasar Iran tana bakin ciki ga duk wani tashin hankali da ya faru a kasashe makwabta tare da bukatar a bayar da mahimanci ga harakokin tsaro da kwanciyar hankali ga dukkanin kasashen dake makwabta da ita.

Rabiei ya tabbatar da cewa Iran kamar ko wani lokaci a shirye take ta bayar da gudumuwarta ga ‘yan uwanta na kasar Iraki, sannan ya tabbatar da cewa duk wata makarkashiya da rohoton kage ba zai raba ‘yan uwantakar dake kasashen kasashen Iran da Iraki ba.

Kakakin gwamnatin jamhoriyar musulinci ta Iran ya yi ishara dacewa Al’ummar kasar Iraki za su fi hanyoyin doka da tafarkin dimokaradiya domin neman hakokinsu da kuma magance matsalolin da suke fama da shi, sannan ya bukaci al’ummar kasar ta Iraki da su kasance masu basira wajen dakile makircin makiya da masu muguwar aniya na neman ci gaba da zubar da jini a kasar.

A cikin ‘yan kawanakin da suka gabata, al’ummar kasar Iraki a birnin Bagdaza da wasu manyan biranan kasar sun gudanar da zanga-zangar nuna adawar da yadda al’ummar kasar ke rayuwa duk kuwa da tarin dukiyar da Al.. ya horewa kasar, to amma yadda aka yi amfani da zanga-zangar wajen kisan fararen hula da jami’an tsaron kasar ya tabbatar da cewa akwai hanun makiya daga kasashen waje a rikicin kasar.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu