Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ne ya bayyana muradin kasar tasa na bunkasa alakar soja da fasaha ta zamani da kuma ayyukan jin kai da ceto, da kasashen nahiyar Afirka.

Shugaba Putin ya bayyana haka ne a wata hira da kamfanin dillancin labarun Rasha na “TASS” a jajiberin taron da za a yi a tsakanin Rashan da kasashen nahiyar Afirka.

Taron wanda za a bude shi a yau Laraba zuwa gobe Alhamis a yankin Sochi, zai mayar da hankali ne akan bude sabon shafi na alaka a tsakanin Rasha da nahiyar Afirka.

Sai dai shugaban na kasar Rasha ya ja kunnen kasashen Afirka akan yakin tattalin arziki da yake gudana a tsakanin manyan kasashen duniya, da yadda zai iya yin tasiri akan nahiyarsu.

Har ila yau, shugaban na kasar Rasha ya ce kasarsa za ta saurari shawarwarin da kasashen nahiyar ta Afirka za su gabatar dangane da yadda za a bunkasa alaka a tsakanin bangarorin biyu.

Vladimir Putin ya kuma yi tuni akan rawar da Rasha ta taka a baya wajen fada da mulkin mallaka da tsarin wariya a cikin nahiyar,wanda zai iya zama matashiya akan cigaba da alakar bangarorin biyu.