A karon farko shugaba Vladimir Putin ya karbi bakuncin shugabannin kasashen Afirka a taron hadin gwiwa tsakanin Rasha da Afirka da nufin bunkasa kasuwanci da tattalin arziki a tsakanin nahiyoyin biyu.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya habarta cewa kasashen Nijar da Rasha sun sanya hanu kan wata yarjejeniya na sayarwa kasar Nijar jiragen yaki masu saukar angulu 12, ministan harakokin Nijer Kalla Ankourao ya bayyana cewa kasar ta cimma matsaya da kasar Rasha na sayarwa kasar wadannan jirage wadanda za su taimakawa kasar wajen yaki da take yi da 'yan ta'adda.

A bangare guda kuma kasar Rashan ta kula yarjejeniyar aiki tare da kasar Eritrea kan gina mata makamashin nukiliya da nufin samar da wutar lantari da kuma ayyukan da suka shafi ayyukan kiyon lafiya, kamar yadda kuma aka kulla irin wannan yarjejeniya tsakanin kasar Rashan da kasar Afirka ta kudu.

Moscow dai na neman yin tasiri a wannan nahiya ta Afirka da tuni China da kasashen yammaci na Turai suka dade suna hulda a tsakaninsu.

Wakilai sama da 3000 da ke halartar taron na yini biyu da ke gudana a birnin Sochi, za su yi mahawara domin cimma yarjeniyoyi akan batutuwan da suka shafi makamashin nukiliya da hako ma'adinan karkashin kasa.