Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rauhani ya bayyana cewa, samuwar sojojin kasar Siriya a kan iyakar kasar daga arewa, kuma kan iyakam dakasar Turkiya shi ne kadai maganin matsalolin tsaro da ake fama da su a yankin a halin yanzu.

Tashar talabijin ta Presstv a Tehran ta nakalto shugaban ya na fadar haka a yau, ya kuma kara da cewa ya zama wajibi ga bangarorin da abin ya shafa su taimaka wajen ganin haka ya faru.

Rauhani ya kara da cewa yakamata kungiyar kurdawa ta YPG su dauki cewa kasar Siriya kasarsu ce, sannan su yi aiki tare da gwamnatin kasar Siriya don dawo da zaman lafiya a yankin nasu.

A cikin wannan makon da muke ciki ne dai gwamnatin kasar Turkiya ta kutsa cikin arewacin kasar Siriya don murkushe mayakan kungiyar YPG wadanda take ganin barazana ce ga zaman lafiya a kasar Turkiyya.

Shugaban Rauhani ya ce sun tattauna wannan batun da gwamnatin kasar turkiya a cikin watan day a gabata, sannan kafin haka dole ne sojojin kasar Amurka su fice daga kasar Siriya kwata-kwata, sannan a dawo da ikon gwamnatin kasar Siriya a dukkanin yankunan kasar.

Gwamnatin kasar Turkiya dai tana daukar kungiyar Kurdawa ta YPG kungiyar yan ta’adda ce, kuma rashe ce daga kungiyar PKK da kurdawa masu son ballewa daga kasar.