Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya bayyana matsin lambar makiyan kasar da cewa bai yi nasara ba.

Tashar presstv ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake ganawa da ministan ma’aikatar tattara bayanan asiri da kuma manyan jami’ai na ma’aikatar a yau a birnin Tehran, shugaba Rauhani ya bayyana cewa, duk da irin matakan matsin lamba da kasashen da ke kiyayya da kasar suke ta dauka domin durkusar da ita, amma har yanzu hakarsu ba ta cimma ruwa ba.

Ya ci gaba da cewa, a halin yanzu an wuce lokacin da wata kasa za ta dora mahangarta da siyasarta a kan Iran, domin kuwa a yanzu ita kasa ce mai cin gishin kanta kuma mai cikakken iko da ‘yanci na siyasa.

Shugaba Rauhani ya jinjina wa dukkanin jami’an ma’aikatar tattara bayanan aisri, inda ya ce aikinsu na da gagarumin muhimamnci da matsayi na musamman, wanda shi ne ma ya kara taimaka ma kasar ta kai inda take ahalin yanzu.

Tun bayan zaben shugban Amurka Donald Trump shekaru uku da suka gabata, yake ci gaba da daukar matakai na matsin lamba da saka takunkumai kan kasar Iran da nufin karya ta baki daya, ko kuma tilsta mata ta bi sharuddan da Amurka ta gindaya mata, inda har yanzu kasar ta Iran take ci gaba da yin turjiya.