Sojojin Indiya Da Pakistan Sun Yi Musayar Wuta A Kan Iyakokin Yankin Kashmir

-KADUNA PRESS.
Sojojin kasashen Indiya da kuma Pakistan sun yi musayar wutar atilari da kuma bindgogi a yankin Kashmir a ranar Asabar.

Jaridar Dawn Daily ta kasar Pakistan ta nakalto majiyoyin gwamnatocin biyu suna tabbatar da labarin.

Inda Raja Farooq premier mai kula da Aza Jamu da Kashmir yana cewa sojojin Indiya sun bude wutar atilari a kan yankin Kashmir da ke karkashin ikon Pakistan, inda akalla mutane 6 suka rasa rayukansu, sannan a bangaren Indiya ma wasu mutane akalla biyu sun rasa rayukansu sannan wasu sun samu raunuku.

Farooq ya kara da cewa yankunan da abin ya fi shafa sun hada da Muzaffarabad da kuma kwarin Neelum.

Labarin ya kara da cewa mutanen garin Chakothi a yankin Kashmir da ke karkashin ikon kasar Pakistan a sun kaurace wa gidajensu saboda musayar wutar.

Mutanen yankin Kashmir ta kasar Indiya, wadanda mafi yawansu musulmi ne suna son ballewa daga kasar Indiya don gujewa mamayar mabiya addinin hindu masu rinjaye a kasar Indiya tun shekara ta 1947 bayan samun ‘yeacin kai.

Kasashen Indiya da Pakistan sun shiga yaki har sau biyu tun bayan samun ‘yancin kai dangane da yankin na Kashmir.
-J.S.A
-KNPRSCD 06.
-Kaduna Press.