A daren laraba da ya gabata ne shugaban da ya gabata ne jamhoriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rouhani ya gana da ministan harakokin wajen kasar Afirka ta Kudu Naledi Pandor inda ya bayyana wajibcin bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu tare da ta tabbatar da cewa hakan zai amfani al'umomin kasashen biyu.

Kafar watsa labaran fadar shugaban kasar Iran ta habarta cewa a yayin wannan ganawa, shugaba Rouhani ya bayyana kasar Afirka ta kudu a matsayin kasa mai mahimancin gaske a nahiyar Afirka wacce take da albarkatun karkashin kasa da kuma al'umma mai ilimi, sannan ya tabbatar da cewa alakar dake tsakanin Iran da Afirka ta kudu alaka ce ta amintaka.

Shugaba Rouhani ya yi ishara kan takunkumin da kasar Amurka ta kakabawa kasar Iran bayan ficewarta daga yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran, inda ya ce matakin hukumomin Washington din zai cutar da kowa da kowa, ciki kuwa harda kasar Amurka.

Har ila yau shugaba Rouhani ya bayyana cewa dukkanin abokanin Iran a duniya ciki harda kasar Afirka ta kudu sun bayyana matsayarsu kan takunkumin zalincin da kasar Amurka ta kakabawa kasar Iran tare da bayyana shi a matsayin abinda ya sabawa dokar kasa da kasa.

A nata bangare ministan harakokin wajen Afirka ta kudu Naledi Pandor ta bayyana mahimancin alakar dake tsakanin kasashen biyu, tare da cewa kasarta a shirye take ta fadada alaka da jamhoriyar musulinci ta Iran a dukkanin bangarori.
Ministan ta yi ishara kan ci gaba da kasancewar Iran a yarjejeniyar nukiliyar da ta cimma da kasashen Duniya, sannan ta bukaci kasar Amurka da ta dawo cikin yarjejeniyar, sannan ta dagewa kasar Iran takunkumin da ta kakaba mata.