Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani ya bayyana cewa kyautata dangantaka da kasashe makobta na daga cikin manufofin jumhuriyar musulunci ta Iran mai muhimmanci.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Litinin a lokacinda yake ganawa da tokoransa na kasar Armenia shugaba Armen Sarkissian a birnin Yerevan babban birnin kasar.

Dr Ruhana ya isa birnin Yerevan ne a jiya don halattar taron kungiyar raya tattalin arziki na Eurasian Economic Union (EAEU).

Banda haka shugaba Ruhani ya bayyana shigar kasar Iran cikin kungiyar (EAEU), yana da matukar muhimmanci don wata dama ce gay an kasuwan kasashen kungiyar su amfani da juna a fagage da daman a tattalin arziki.