A ranar Litinin da ta gabata ce kamfanin “Mara Group” na kasar Ruwanda ya kaddamar da wayoyin salula kirar Afurka a karon farko a birnin Kigali.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa wayoyi guda biyu ne kamfanin ya fara kerawa a halin yanzu, kuma sune “Mara X” da Mara Z”.

Banda haka shugaban kamfanin, Ashish Thakkar ya fadawa Reuters cewa ana iya kwatanta kwarinsu da wayoyin kamfanin Samsung, sannan suna amfani da Andrio a matsayin tsarin da ke sarrafa ayyukansu.

Har’ila yau farashin ko wanne daga cikinsu zai kama dalar Amurka $190, ko Franc 175,750 na Ruwanda, da kuma dalar Amurka $130, ko kuma Franc 120,250 na Ruwanda.

Thakkar ya kara da cewa suna kera dukkan sassan wayoyin, wadanda suka fi dubu guda a cikin kasar Ruwanda, sannan suna da karfin samar da wayoyi dubu goma a ko wace rana.