A ranar Litinin da ta gabata ce kamfanin “Mara Group” na kasar Ruwanda ya kaddamar da wayoyin salula kirar Afirka a karon farko a birnin Kigali.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa wayoyin guda biyu da kamfanin ya fara kerawa a halin yanzu, sune “Mara X” da Mara Z”.

Baya ga hakan,shugaban kamfanin wayar salulan Mista Ashish Thakkarya fadawa kamfanin dillancin labaran reuters cewa ana iya kwatanta ingancin wayoyinda wayoyin kamfanin Samsung, sannan suna amfani da Andrio a matsayin tsarin da ke sarrafa ayyukansu.

Har’ila yau farashinsu ko wanne daga cikinsu zai kama dalar Amurka $190 ko franc 175,750 na Ruwanda, da kuma dalar Amurka $130 ko kuma Franc 120,250 na Ruwanda.

Thakkar ya kara da cewa suna kera dukkan sassan wayoyin, wadanda suka fi dubu guda a cikin kasar Ruwanda, sannan kamfanin da karfin samar da wayoyi dubu goma a ko wace rana.