Sayyid Hassan Nasrullah Ya fadi haka ne a lokacin da yake bayani a zaman makoki na zagayowar shahadar Imam Hussaini (As) a kudancin Dahiya, dake birnin Beirut ta kasar Labanon, da yake ishara game da janye goyon bayan da Amurka take bawa kurdawan kasar Syria a rana tsaka ya nuna cewa kukan kurciya ne ga duk wanda ya dauki kasar Amurka a matsayin uwar daki.

Ya ci gaba da cewa Amurka ba abar dogaro ba ce domin hatta kawayenta ma ba su tsira daga sharrinta ba, kuma basu da wata kima a wajenta, don haka duk wanda ya dauke ta a matsayin uba to zai mutu maraya.

Daga karshe ya bayyana cewa tun ba yau ba jagoran juyin musulunci na kasar Iran Ayyatullah sayyid Ali Khamina’i ya fadi cewa kada a tattauna da Amurka domin ba zai yiyu a amince da ita ba.