Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

SHAHADAR IMAM HASSAN (a.s)

ZAMAN JUYAYIN SHAHADAR IMAM HASSAN ALMUJTABA A KADUNA...

-KADUNA PRESS.

Da'irar kaduna ta shirya kuma ta gabatar da zaman makokin Imam Hassan almujtaba (a.s) a cikin garin na kaduna.
Malam Aliyu B/Ruwa ne ya gabatar da jawabi a muhallin,
Inda ya dauki tsawon lokaci yana gabatar da jawabi a muhallin, Malamin ya fara jawabine akan rayuwar Imam ta yadda ya tabo janibobi daban-daban na rayuwar dan uwansa Imam Hussain da kuma mahaifiyarsa Sayyida Zahra da Imam Ali da kakansa Manzon Allah (s.a.w).

Malamin ya nuna cewa baba yadda za'ayi a ambaci rayuwar Imam Hassan ba tare da an ambato wadannan bayin Allah din ba, domin rayuwar sa ta ta'allaka ne da tasu, idan ana da bukatar ambatar dayan cikinsu to sai an ambato sauran.

Shehin malamin ya bayyana yadda Imam Hassan yake da cikakken hakuri na kin-karawa, ya kuma bayyana karatunsa da kaifin basirarsa.

Daruruwan 'yan uwa maza, mata, manya da yara almajiran Sheikh Zakzakiy daga sassa daban-daban na da'irar ta kaduna ne suka samu daman halartar muhallin taron.
An fara kuma an kammala taron lami-lafiy.

-KNPRSCD 06.
-Kaduna Press.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu