Bayan kwanaki 6 da kutsawar sojojin kasar Turkiya cikin kasar Siriya, sojojin kasar ta Siriya da kawayenta sun karbi iko da wasu yankunan arewa masu gabacin kasar tare da samun tarbar mutanen wadannan yankuna da dama.

A ranar 9 ga watan Oktoba da muke ciki ne sojojin kasar Turkiyya suka fara kutsawa cikin arewacin kasar Siriya da sunan yakar kungiyar kurdawa da take dauke da makamai a yankin.

Kafin haka dai sojojin kasar Amurka wadanda suka dade suna mamaye da yankin sun janye, wanda ya nuna cewa kasar Turkiyya ta sami goyon bayan Amurka kafin ta fara wannan kutsen.

Banda haka shugaban kasar ta Amurka Donal Trump ya rubuta a cikin shafinsa na tweeter kan cewa lokaci yayi wanda kasar Amurka zata janye sojojinta daga yake-yake wadanda basu da iyaka.

Bayan fara kutsen ne mutanen yankin arewa maso gabacin kasar ta Siriya suka bukaci sojojin gwamnatin kasar su shiga yankin don karesu daga hare-haren sojojin kasar Turkiya.

Daganan da tare da bata lokaci ba sojojin suka amsa amince da bukatar, sannan suka shiga garin Hasasa inda suka sami kekyawar tarba daga mutanen garin da kuma wasu yankuna da dama kusa da shi.

Kafin haka dai sojojin kasar ta Siriya sun cimma yerjejeniya da kungiyoyin kurdawa wadanda suke iko da wadannan yankuna kafin kutsawar sojojin na Turkiyya.

Samuwar sojojin gwamnatin kasar Siriya a wadannan yankuna na kasar Siriya dai yana da matukar muhimmanci, saboda dalilai kamar haka.

Na farko: Sojojin kasar suna ganin kare mutanen kasar daga makiyansu nauyi ne da yarataya a wuyansu, wanda kundin tsarin mulkin kasar ya dora masu.

Sannan tarbar da suka samu daga wajen mutanen wadannan yankuna ya tabbatar da hadin kai da ke tsakanin mutanen yankin wadanda suka hada da yan kabilar Qurdawa da kuma Larabawa da kuma sojojin kasar.

Na biyu: Sojojin Siriya sun tabbatar da ikon gwamnatin shugaba Bashar Al-asad a wadan nan yankin bayan da wasu kasashe, daga ciki har da kasar Amurka da kawayenta suka yi kokarin kwace yankin daga hannun gwamnatin kasar.

Sai abu na ukku: Shigowar sojojin Siriya a wadannan yankuna, ya kawo karshen ikon da kungoyoyin yan ta’adda wadanda suke iko da yankin kimani shekaru 9 da suka gaba. Wadanda suke samun taimakon kasashen Amurka da kawayensu a yankin.

Daga karshen abu na hudu: shi ne, manufar kasar Turkiyya ta kutsawa cikin arewacin kasar Siriya shi ne hana kokarin da sojojin kasar Siriya suke yi na kawo karshen kungiyoyin yan ta’adda wadanda har yanzun suke rike da wani karamin yankina lardin Idlib wanda zai bawa gwamnatin kasar Siriya cikekken iko da lardin. Don Amurka tana daga cikin kasashen da suna nuna damuwarsu da irin nasarorin da sojojin Siriya da kawayenta suke samu a kan yanta’adda wadanda suke iko da lardin Idlib.