Daga karshe Abubakar bagdadi shugaban kungiyar Daesh ya halaka kamar yadda Amurkawa suka ce, harma kungiyar ta bada sanarwan cewa ta zabi Abdullahi Qardashi a matsayin magajinsa.

Sai dai idan muna maganar Abubakar bagdadi da kuma kungiyar ta’addanci ta Daesh, muna iya kallonsu ta mahanga daban-daban, kuma masana sun rubuta abubuwa da dama dangane da rawar da Amurka ta taka wajen samar da kungiyar Daesh karkashin shugabancin Bagdadi.
Sai dai a wannan karon muna son mu yi Magana dangane da bayyanar Daesh karkashin shuwagabancin Abubakar bagdadi da kuma bala’in da ta saukowa mutane a kasashen Asia ta yamma bayan bayyanarsu.

A cikin watan Yunin shekara 2014 ne kungiyar Daesh ta mamaye arewacin kasar Iraqi, sannan a birnin Mosil birni mafi girma a yankin ya bayyana kansa a matsayin khalifa na musulmi a wadannan yankuna.

A cikin shekaru kimani 4 da ya dauka yana iko da wadannan yankuna, mutanen yankin ba za su taba manta da kissan kiyashin da kungiyar Daesh ta yi da sunan addini ba.

Daga cikin ta’asan da Bagdadi ya aikata a arewacin kasar Iraqi, akwai kisan yan makaranta matasa a makarantar horar da sojoji ta sansanin sojojin sama na “Sabaka”, su 1,700 a lokaci guda, don su yan shia’a ne, sannan aka yi masu kabarin gama gari.
Daga nan Bagdadi ya kama mata da yara a yankin a matsayin kuyangu yana saida su tsakanin mabiyansa, sannan mayakansa sun kashe mata da yara a gaban jama’a, tare da raba kansu da jikunannsu, musibar da mutanen kasar Iraqi basu taba ginin irinsa ba.

Wannan halin ya kaiga iyalai da dama suka bar gidajensu suka koma kan tsaunuka don kubutar da rayukansu, inda da dama daga cikinsu sun mutu saboda kishin ruwa da yunwa a can.

Musiba ta biyu wacce Daesh ta jawowa mutane a kasashen yankin Asia ita ce wargajewar tsarin zamnatakewa da kuma khidima wa a wadannan yankuna da kungiyar ta mamaye a kasashen Iraqi da Siriya, inda ta rusa makarantu, da cibiyoyin kiwon lafiya, sannan aka dakatar da ayyukan kiwo da noma a wadannan yankuna.

A halin yanzu daya daga cikin matsalolin da kasar Iraqi take fama da su, bayan an kwace wadannan yankunan daga hannun Daesh, har ya kai ga tashe-tashen hankula na baya-bayan nan, sun hada bacewar wadanan khidimomin da akewa mutanen kasar sanadiyar lalatasu da kungiyar Daesh ta yi.

Banda haka kungiyar ta maida wadannan kasashe baya, na shekaru masu yawa, saboda rusa ci gaban da suka samu a baya.
Daga karshe, sakon shugaban kasar Amurka Donal Trump na cewa sojojinsa sun halaka shugaban kungiyar Daesh Abubakar Bagdadi a ranar Lahadin da ta gabata, don haka kuma yana ganin shi ne gwarzon yaki da kungiyar Daesh, wannan ba haka yake ba ga mutanen kasashen yankin Asia ta yamma. Musamman kasashen Iraqi da Siriya.

Wannan ba don komai ba sai don har yanzun akwai yayan wannan kungiyar a cikin kasashen Iraqi da Siriya da ma wasu kasashen yankin, kuma mutuwarsa a wajen matanen wadanan kasashe, ba a bakin kome ba sai dai an shiga wata marhala ce ta zaluncin da kasashen Amurka da kawayenta suke yi a mutanen wadannan kasashe.