Shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi ya lashe zaben da aka gudanar a kasar da babban rinjaye wanda ya bashi damar ci gaba da shugabancin kasar na wasu shekaru 5.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto hukumar zaben kasar ta Mozambique CNEtana bada sanarwan cewaNyusi ya lashe zaben da kashi 73% na yawan kuri’un da aka kada a zaben ranar 15 ga watan Octoba da muke ciki.

Hukumar zaben CNE ta ce jam’iyyar adawa mafi girma a kasar, wato Renamo ta tashi da kashi 21.88% , na yawan kuri’un da aka kada.

Sannan tuni ta bayyana cewa bata amince da sakamakon zaben ba.