Shugaban Muhammadu Buhari na tarayyar Najeriya ya hana dukkan ministocinsa da kuma maya-manyan jami’an gwamnati fita daga kasar har zuwa lokacinda majalisar dokokin kasar za ta kammala aikin tantance kasafin kudi na shekara ta 2020.

Willie Bassey darakta mai kula da al-amuran watsa labarai na ofishin sakataren gwamnati ne ya bayyana haka a jiya jumma’a. Ya kuma kara da cewa shugaban yana bukatar ministocinsa su jagoranci ma’aikatunsu wajen kare kasafin kudin da aka ware wa ma’aikatun a kasafin kudi na shekara ta 2020 wanda yake gaban majalisar dokokin kasar a halin yanzu.

Har’ila yau labarin ya kara da cewa samuwar ministocin da kuma manya-manyan jami’an gwamnatin zai taimakawa majalisar dokokin kasar gaggauta kammala ayyukansu da suka shafi kasafin kudin.

Sanarwan ta kara da cewa Ministocin da suka sami izinin tafiya kafin wannan sanarwan su sake tuntubar fadar shugaban kasa bayan sun kammala ayyukan da yakama suyi tare da majalisar dokokin kasar kan kasasfin kudaden ma’aikatunsu.

Banda haka sanarwan ta kammala da cewa ministocin da manya-manyan jami’an gwamnati su tuntubi majalisar dokokin kasar don sanin lokacinda yakamata su je majalisar don kare kasafin kudin da aka warewa ma’aikatun.