A safiyar jiya lahadi ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwar cewa sojojin Amurka sun sami nasara kashe shugaban kungiyar yan ta’adda ta Daesh ko IS Abubakar Bagdadi a wani wuri a yankin Idlib na kasar Siriya.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa shugaban ya bayyana haka ne a wani taron yan jarida da ya kira a jiya Lahadi a fadar white house.
Trump ya kara da cewa Abubakar Bagdadi ya tarwatsa kansa ne da boma-bomai wadanda ya yi damara da su a lokacinda ya tabbatar da cewa sojojin Amurka sun rutsa da shi a cikin wata mabuyarsa ta karkashin kasa.
Shugaban ya ce Bagdadi ya tarwatsa kansa ya kuma kashe yayansa guda ukku da suke tare da shi a cikin ramin da aka rutsa da shi.
Trump ya bayyana cewa boma-boman sun tarwatsa jikinsa, amma gwajin DNA da aka yi na wani bangare na jikinsa jim kadan bayan halakarsa ya tabbatar da cewa shi ne.
0 Comments