Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya bar Tehran dazu zuwa birnin Baku na kasar Azerbaijan domin halartar taron kungiyar ‘yan ba-ruwanmu da za a yi gobe Juma’a.

Shugaban Ofishin shugaban kasar Iran, Mahmud Wa’izy ya bayyana cewa; A yayin zamansa a birnin Baku, shugaba Dr. Hassan Rauhani zai gana da takwarorinsa na kasashen duniya daban-daban domin bunkasa alaka a tsakanin kasashen.

Ita dai kungiyar ‘yan ba-ruwanmu an kafa ta ne a 1961 a birnin Belgrade tana kuma da mambobi fiye da 125 da masu sanya idanu 25. A lokacin da aka kafa kungiyar dai ana yin yakin cacar baki ne a tsakanin yammacin turai da tarayyar Soviert domin su nesanta kansu daga rikicin bangarorin biyu.