A karon farko da yake gudanar da Jawabi ga masu zaman dirshin da zanga-zangar neman kawo sauyi a kasar , Shugaban kasar Labnon Michel Aoun yace akwai bukatar ayyukan hadin gwiwa tsakanin gwamnati da Majalisa domin kawo karshen barnar dukiyar gwamnati a kasar
Shugaban Aoun ya tabbatar da cewa ya zama wajibi a hada kai tsakanin gwamnati da Majalisar dokokin kasar wajen aiwatar da gyare-gyaran a bangaren tattalin arzikin kasar ta yadda za a fitar da kasar daga halin da ake ciki.

A wani bangare na jawabinsa, Shugaba Aoun ya ce shi ma ya yi bakin ciki dangane da yadda ake yin barnar dukiyar gwamnati a kasar,duk wadanda suke satar kudin gwamnati dole su fuskanci hukunci, domin babu wata kungiya ko mazhaba ko addini da ta yarda da satar dukiyar gwamnati.

Shugaban kasar ta Labnon ya bukaci a gaggauta aiwatar da gyare-gyaren da aka yiwa tattalin arzikin kasar domin dawo da amincewar al’ummar kasar ga gwamnati, sannan ya ce wannan gyara na a matsayin matakin farko na fita daga matsalar kudi da tattalin arzikin kasar.

Shugaba Aoun ya tabbatarwa al’ummar kasar da cewa shi da kansa zai bi al’amarin domin ganin an tabbatar da gyare-gyaren da aka yi kuma ya bayyanawa al’ummar kasar, lokaci ya yi da za a gudanar da sauyi a kasar, munada wakilai da zai bi diddigin al’amarin, tattaunawa ita ce hanya mafi kyau na ceto kasar daga halin da take ciki a yau.

A karshe, shugaban na Labnon yace a shirye yake ya zauna kan tebiri guda da wakilan masu adawa, inda y ace lokaci ya yi da za a rusa duk wani tunani na bangaranci da kabilanci, tunanin bangaranci shi ne babbar matsalarmu a yau, yayin da a bangare guda matsalar dukiyar gwamnati ta ratsa kwakwalanmu da kashishiwanmu.