A dazu ne dai shugaban kasar ta Rasha Putin ya isa birnin Riyadh domin fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu,inda ya sami tarba ta hanyar shirya masa fartetin girmamawa a filin saukar jiragen sama.

A jiya Lahadi shugaban kasar na Rasha ya gabatar da taron manema labaru a birnin Moscow inda ya yi tir da harin da aka kai wa cibiyoyin kamfanin mai na Aramco na Saudiyya, a lokaci guda kuma yana mai jaddada muhimmanci rawar da Iran take takawa a cikin wannan yakin.

A yayin ziyarar tasa a Saudiyya shugaba Putin zai gana da sarki Salamn Bin Addulaziz da kuma yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salaman, domin tattauna alaka a tsakanin kasashen biyu da kuma abubuwan da suke faruwa a gabas ta tsakiya.

Kasar Rasha dai tana kokarin zama mai shiga tsakani ne a tsakanin kasashen yankin gabas ta tsakiya.