Shugaban kasar ta Syria Basshar Assad wanda ya gabatar da jawabi akan shigar da sojojin Turkiya su ka yi cikin kasar sannan ya kara da cewa:Syria za ta mayar da martini akan wuce gona da irin na Turkiya.

Shugaba Assad ya bayyana haka ne a yayin da yake karbar bakuncin shugaban majalisar koli ta tsaron kasar Iraki, Falih al-Fayyadh, a birnin Damascuss

Falih al-Fayyadh ya isar da sakon Firaministan kasar Iraki ne Adil Abdulmahadi zuwa ga shugaban na kasar Syria

Basshar Asad, ya kara da cewa; A tsawon tarihi kasashen waje suna da kwadayin shiga cikin kasashen wannan yankin, kuma harin da Urdugan ya kai wa Syria yana cikin wadannan irin hare-haren.

A nashi gefen, Al-Fayyadh ya bayyana cewa; Kasashen Iraki da Syria za su cigaba da yin aiki tare da juna a fuskoki daban-daban domin tabbatar da tsaro.