Shugaban kasar Turkiya Rajab tayyeed Urdugan ya bayyana cewa ba zai gana da tawagra kasar Amurka karkashin mataimakin shugaban kasa Mike Pence ba.

Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaba Ordogan yana fadawa Sky News cewa tawagar za ta gana da tokororinta a kasar, amma shugaban kasar ba zai gana kowa ba in banda shugaban kasar taAmurka.

Shugaan kasar Amurka Donal Trump ya aike da tawaga karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasar Mike Pence don ganawa da Urdogan kan dakatar day akin day a fara a kasar Siriya.

Amma daga baya an nakalto jami’in watsa labarai na shugaban Fahrettin Altun ya rubuta a cikin shafinsa na tweeten kan cewa shugaban zai gana da tawagar.

Tun kimani kwanaki goma da suka gabata ne gwamnatin kasar turkiyya ta fara mamayar wasu yankuna a kasar Siriya da sunan yaki da kurdawa wadanda suke iko da yankunan, wadanda yake daukarsu a matsayin yan ta’adda.