Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Shugaban majalisar kasar Iran ya soke ziyarar da zai kai kasar TurkiyaDr Ali Larijani shugaban majalisar shawarar musulunci ta kasar Iran ya samu goron gayyata ne daga takwaransa na kasar Turkiya domin halatar taron yan majalisu da za a yi a birnin santanbul.

Sai dai ya soke kai ziyarar jim kadan bayan kaddamar da hare-haren soji da Turkiya ta yi a Arewa maso gabashin kasar Siriya.

A jiya ne shugaban kasar Turkiya Dayyib rajab Urdogan ya fara kai harin soji kan sansanin mayakan Kurdawa dake Arewa maso yammacin kasar Syria, wanda kafin haka sai da shugaban kasar Rasha Vlademir Putin ya kira yi takwaransa na Turkiya da ya yi dogon tunani kafin ya kai harin.

Rahotanni sun nuna cewa daruruwan mutane ne suka fara tserewa daga gidagensu domin neman mafaka, bayan hare -haren ta sama da dakarun kasar Turikiya suka fara kai wa a garin Aini Birif dake Arewa maso yammacin kasar Syria.

Tuni dai kasashen duniya suka fara yin tir da wannan hari, inda kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da zaman gaggawa domin duba irin mataken da za’a dauka game da harin na Turkiya kan mayakan kurdawa a kasar Syria.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu