Da ya ke jawabi a gaban gammayyar majalisar Dattawa da wakilai ta Nigeria , Buhari ya ce an yi hasashen samun riba ta naira tiriliyan 2.64 daga albarkatun man fetur, sai kuma naira tiriliyan 1.81 daga bangarorin da ba na fetur da dangoginsa ba. Kuma za a kashe naira tiriliyan 2.45 wajen biyan basussuka na cikin gida da waje.

A cikin kasafin kudin an ware wa harkokin tsaro naira bilyan 110, yayin da aka ware naira bilyan 37.83 ga bangaren hukumar raya yankin Arewa maso Gabashin kasar. Ya kara da cewa an samu cikas a kasafin 2019, saboda jinkirin da aka yi kafin a amince da kasafin da kuma rashin tara makudan kudaden harajin da aka yi hasashen tarawa a shekara ta da ta gabata 2018.

A nata bangaren majalisar dokokin Nigeria ta sha alwashin kammala komai tare da mika kasafin kudin da shugaban kasa ya gabatar mata na Naira Triliyan 10.33 a makon farko na watan Disamba mai zuwa.