Shugabannin kasashen Afrika da dama sun hallara a kasar Rasha domin halartar taron Rasha-Afrika karo na farko a tarihi, wanda zai samu halartar shugabanni kimanin 47 na kasashen Afrika.

Shugaba Putin na Rasha ne dai ya shirya taron, wanda zai karbi bakuncinsa a birnin Sochi na kasar ta Rasha daga gobe Laraba zuwa ranar Alhamis mai zuwa.

Babbar manufar taron dai ita ce kara bunkasa alaka tsakanin kasashen Afrika da Rasha a dukkanin bangarori na siyasa, kasuwanci, tattalin arziki, tsaro, noma da sauransu.

Kasar wadda ta samu gagarumin ci gaba ta fuskar noma, za ta iya taimaka kasashen Afrika da dama ta fuskar noma, kamar yadda ita ma za ta ci gajiya daga kasashen Afrika wajen sayar da kayayyakin da take samarwa, ta fuskar noma da kuma kayan aiki ta fuskar soji da tsaro.

Gwamnatin Amurka ta yi kakkausar suka kan wanann yunkuri da Rasha take yi na fadada alakarta da kasashen nahiyar Afrika, inda Amurka ke kallon hakan a matsayin wani sabon salon a dubara domin mamaye arzikin Afrika, inda ta sha alwashin ganin ta kawo cikas ga abin da ta kira yunkuri mamaye Afrika da kasashen China da Rasha suke yi.