Rahoton dagidan talbijin din kasar Syria ya watsa ya nuna cewa wani rikicn ya barke tsakanin sojojin kasar da kuma na kasar Turkiya a garin Ra’asul Aindake kan iyaka a Arewa maso gabashin kasar Syria, kuma an kashe wani sojan Turkiya daya tare da jikkata wasu guda biyarna daban kamar yadda majiyar sojojin kasar turkya ta sanar.

Daga lokacin fara mamayar da kasar Turkiya ta yi a kasar Syria garin Ra’asulAin ya ci gaba da zama a mtsayin inda aka ta gwambza yaki tsakanin dakarun kurdawana kungiyar Syria Democratic , kuma yana da muhimmancin sosai saboda kasancewarsa kusa da iyakarsu da kasar Turkiya.

Ya zuwayanzu an jibge dakarun sojin kasar Syria a kauyuka Sabadiya, jamiliya, da sauran su dake Arewa masu yammacin garin Haska, wanda haka ya ba su damar kusantowa kusa da iyakokin kasar ta kasar Turkiya.