Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya ruwaito rundunar tsaron kasar Siriya na cewa bisa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatin kasar da shuwagabanin kurdawan siriya, dakarun tsaron kasar sun kutsa garin Ainul-Arab da kurdawa ke kira da kubani.

Bayan hare-haren da dakarun kasar turkiya suka kaddamar a kan yankunan kurdawa na arewacin kasar ta Siriya, dakarun kurdawa sun bukaci gwamnatin siriya da ta karbi iko da yankunan kan iyakar arewacin kasar, sannan ta kare su daga hare-haren da gwamnatin Turkiya ta kaddamar a kansu.

Bisa yarjejeniyar da aka cimma dai, Sojojin kasar Siriya za su karbi iko da dukkanin yankunan dake kan iyakar kasar da Turkiya, sannan kuma za su hada kai domin dakile hare-haren da kasar turkiya ke kaiwa kan al'ummar kasar 'yan kabilar kurdawa.