Majiyar sojojin kawance masu yaki da da’addancina kasar Siriya karkashin jagorancin Amurka ta bada sanarwan cewa ta fice daga garin Raqqa da kuma Tabqah, har’ila yau ta fice daga kamfanin sarrafa siminti na Lafarge daga Arewacin kasar Siriya a jiya Laraba.

Labarin ya kara da cewa tun ranar 16 ga watan Octoban da muke ciki ne sojojin Amurka da kawayenta suka fara jenyewa daga arewacin kasar Siriya wanda ya budewa gwamnatin kasar Turkiyya damar fara mamayar kasar daga ta Siriya daga arewacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto kakakin kawancen na Amurkan Colonel Myles B.

Caggins yana fadar haka a shafinsa na tweeter.

Har’ila yau janyewar Amurkan ya bawa sojojin gwamnatin kasar Siriya damar sasantawa da wasu kungiyoyi da dauke da makamai a wadannan yankunan, wanda ya bawa sojojin damar shiga wadannan yankuna don kare su daga hare-haren sojojin Turkiyya.