Dakaruntsaronkasar Mali sun sanar da kashe ‘yanbindigakimanin 50 da kuma kubutar da sojojin da akayi garkuwa da su, bayan wani kazamin harin da aka kai sansanonin su guda biyu a watan da yagabata.

KamfanindillancinlabaranFaransana AFP yaruwaitorundunartsaronkasar Mali nacewaSojojinkasar sun samunasararkashe ‘yanbindigakimanin 50 da kumajikkatawasu 30 nadaban a wanisumame da sukakaimobayarsu.

Sanarwar ta ce an lalatamakamaimasuyawana ‘yanbindigar tare kuma da kubutar da sojoji 36 dagasojojikusan 60 da sukabatayayinwaniharin da ‘yanbindigasukakaisansanoninsojanbiyu a watanSatumbar da yagabata, lamarin da yasanyaiyalansugudanar da zanga-zangananemansaninhalin da sukeciki.

A harin da ‘yanbindigarsukakaiwasojinna Mali a watanSatumbar da yagabata, sun kashesojoji 38, sannanwasukimani 60 nadaban sun bace.

Harinnawatan da yagabata, shi ne mafi muni da ‘yanbindigarsukakaiwaSojojin Mali, tun bayan tashin hankalin da ya barke a kasar a shekarar 2012, lokacin da Yan bindigar suka kwace boren da Abzinawa suka yi.

Wannan ya sanyakasar Faransa ta girke dakaru 12,000 a kasar ta Mali, da kuma jagorancin kafa rundunar G5 Sahel wadda ta samu sojoji daga kasashen Mauritania da Mali da Nijar da Chadi da kuma Burkina Faso domin magance hare haren na ‘yanbindiga a yankin.