A Yau Litinin ne sojojin kasar ta Syria su ka isa yankunan Kurdawa da suke kusa da iyakar kasar Turkiya, domin mayar da martani akan hare-haren da sojojin na Turkiya suke kaiwa.

Kungiyoyin Kurdawa masu dauke da makamai a yankin sun kulla yarjejeniya da gwamantin Damascuss akan kafa sansanonin domin fuskantar hare-haren na Turkawa.

Kamfanin dillancin labarun AFP ya ambato cewa; Sojojin na Syria sun kafa sansanonin nasu ne a kusa da garin Tal-Tamr, inda mutanen garin su ka yi maraba da su.

Da akwai nisan kilo mita 30 zuwa garin Ra’as-Ayn dake gundumar Hasaka da ake yaki tsakanin sojojin Turkiya da mayakan Kurdawa