Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Sojojin Syria SunKafa Sansanoni A Kusa Da Iyaka Da Kasar TurkiyaA Yau Litinin ne sojojin kasar ta Syria su ka isa yankunan Kurdawa da suke kusa da iyakar kasar Turkiya, domin mayar da martani akan hare-haren da sojojin na Turkiya suke kaiwa.

Kungiyoyin Kurdawa masu dauke da makamai a yankin sun kulla yarjejeniya da gwamantin Damascuss akan kafa sansanonin domin fuskantar hare-haren na Turkawa.

Kamfanin dillancin labarun AFP ya ambato cewa; Sojojin na Syria sun kafa sansanonin nasu ne a kusa da garin Tal-Tamr, inda mutanen garin su ka yi maraba da su.

Da akwai nisan kilo mita 30 zuwa garin Ra’as-Ayn dake gundumar Hasaka da ake yaki tsakanin sojojin Turkiya da mayakan Kurdawa

Post a Comment

0 Comments

Close Menu