Shugaba Muhammadu Buhari ya fadi haka ne a jiya laraba a lokacin rantsar da sabbin mabobiin kwamatin dake bawa shugaban kasa shawara kan tattalin arziki da ya kunshi mutane 8 karkashin jagorancin Profeso Doyin Salami.

An fitar da sabbin tsare-tsaren da za a iya cin gajiyarsu a mafi karancin lokaci, kuma ya bukaci kwamitin ya mai da hankali wajen tattara sahihan alkaluma da za su yi daidai da hakikanin abin da ke faruwa a kasar.

Har ila yau ya kara da cewa ya kamata ya mayar da hankali wajen tattara alkaluma tun daga tushe, domin mafi yawancin alkaluman da ake fitarwa game da yanayin tattalin arzikin kasar suna fitowa ne daga bakin duniya ko kuma Asusu bada lamuni na duniya IMF da dai sauran wasu kungiyoyi na kasahen waje.

Ka kara da cewa wasu daga cikin kididdigar da ake fitarwa game da Nigeria alkaluma ne da suka yi kama da kirgar dokin rano don ba su da alaka ko kadan da hakikanin abin da ke faruwa kasa.

Daga karshe ya bayyana cewa wannan lamari ne mai tada hankali dake nuna cewa bamu da cikakkiyar masaniya kan abin da ke faruwa a kasarmu, kuma za mu iya yin shiri na gaske ne idan muna da ingantattun bayanai a hannunmu.