Sabuwar alkaliyar alkalan kasar Sudan ta jadadda wajibcin yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annuti da kuma wadanda suke da hannu a kisan masu zanga-zanga.

Jaridar Al-tarbiyu ta kasar Sudan ta nakalto Sabuwar alkaliyar alkalan kasar Sudan Tajussir Ali Al-habar na cewa duk wadanda suka aikata laifi a kowane bangare na ma'aikatun kasar za su fuskanci hukunci.

Yayin da take ishara kan Sojojin da suka kashe masu zanga-zangar neman sauyi a kasar, ta ce a halin da ake ciki ana ci gaba da bincike kan lamarin kuma tuni aka gabatar da su a gaban kotu.

A ranar 19 ga watan yulin da ya gabata, kwamitin likitocin kasar Sudan ya sanar da cewa daga lokacin da aka fara zanga-zanga kin jin gwamnati a watan Disamban 2018 zuwa wannan lokaci an kashe mutane 246 tare da jikkata wasu dubu daya da 353 daga cikin fararen hular kasar.