Gwamnatin rikon kwarya ta kasar Sudan da kungiyoyin 'yan tawayen kasar sun cimma matsaya na tattaunawa domin cimma matsayar karshe na kawo karshen yaki a yankin Darfur da wasu yankuna biyu na daban.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya habarta cewa a wannan Litinin ne ake sa ran bangarorin biyu za su sanya hanu kan yarjejeniyar siyasa bisa jagorancin shugaban kasar Sudan ta kudu Salva keir da kuma sa ido na tawagar kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Juba.

Rahoton ya ce gamayar kungiyoyin 'yan tawayen na Sudan na daga cikin gamayar kungiyoyin neman sauyi da 'yanci na kasar da suka jagoranci gwagwarmayar kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Omar Al-Bashir, kuma tun a ranar alhamis din da ta gabata ce aka fara wannan tattaunawa ta sulhu bisa shiga tsakanin shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Keir.

Bisa yarjejeniyar farko da aka cimma dakarun bangarorin biyu za su dakatar da ayyukan soja, domin samun damar shigar da kayan agaji ga fararen hula dake yankin da ake rikici.

Tun a watan Satumbar da ya gabata ce sabuwar gwamnatin rikon kwarya ta Sudan ta fara tattaunawa da kungiyoyin 'yan tawayen kasar a birnin Juba na kasar Sudan ta kudu da nufin cimma yarjejeniyar kawo karshen yaki a kasar.