‘Yan adawa masu dauke da makamai a Sudan ta Kudu, sun yi barazanar kauracewa shirin kafa gwamnatin hadin kasa da za’ayi a watan gobe, kamar yadda kungiyar SPLM-IO da tsohon mataimakin shugaban kasar Reak Mashar ke jagoranta ta sanar.

A bara ne bangarorin dake rikici a kasar, Reik Machar da kuma Salva Kirr, suka sanya hannu a kan yarjejeniyar kawo karshen rikicin da aka kwashe shekaru biyar ana yi a kasar.

A ranar 12 ga watan Nuwamba mai zuwa ne ya kamata a ce bangarorin biyu sun cimma yarjejeniya ta kafa gwamnatin hadaka, sai dai bangaren ‘yan adawan na SPLM-IO, ya ce ba zasu shiga shirin kafa gwamnatin ba, muddin ba’a aiwatar da aiki da gaba dayan abubuwan da yarjejeniyar zaman lafiya ta cimma ba.

Batutuwan da bangarorin ke da sabani akai har yanzu sun hada da batun yadda za’a samar da tsaro, da adadin yankuna da iyakokinsu, da kuma canza kundin tsarin mulkin kasar, wanda hakan ya kawo tsaiko, har aka dage shirin kafa gwamnatin da watannin shida.