Ministocin harakokin wajen kasashen Iran, Rasha da Turkiya sun gudanar da taro a daren jiya Talata a birnin Ganeva, inda a karshen taron suka fitar da sanarwar hadin gwiwa na kare hurumi da kuma 'yancin kasar ta Siriya

Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa wannan taro da aka gudanar a jiya talata ya samu halartar ministan harakokin wajen kasar Iran Muhamad Javad zarif da takwaransa na kasar Rasha Sargei Lavrov gami da takwaransu na kasar Turkiya Mevlüt Çavuşoğlu.

A yayin wannan taro, ministocin harakokin wajen kasashen uku sun tattauna kan rikicin kasar siriya da kuma abinda ke gudana na wannan lokaci, inda a karshen taron suka fitar da sanarwar hadin gwiwa na tabbatar da kare hukunci da kuma 'yancin kasar ta Siriya a matsayin dunkulalliyar kasa mai 'yanci.

Har ila yau taron ya yi maraba da kafa kwamiti na yiwa kundin tsarin milkin kasar ta Siriya kwaskwarima wanda zai bawa ko wani bangare shiga harakokin siyasa a dama da shi.

A karshe mahalarta taron sun tabbatar da cewa rikicin siriya ba za a iya magance shi ta hanyar karfin soja ba domin haka ya zama wajibi ayi aiki da kudirin kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Diniya mai lamba 2254 domin magance rikicin kasar ta hanyar siyasa.