Cikin wani jawabi da suka fitar a daren laraba, dakarun kurdawa na kasar Siriya SDF sun yawabawa kasar Rasha kan rawan da ta taka na dakatar da hare-haren da kasar Turkiya ke kaiwa yankunan arewacin kasar.

Dakarun kurdawan Siriya na SDF sun sanar a daren cewa matakan da kasar Rasha ta dauka na shiga tsakani da kuma dakatar da haren haren da kasar Turkiya ke kaiwa yankunansu na arewecin kasar abin a yaba ne.

Bayan tattaunawa da sa'o'i 6 tsakanin shugabanin kasashen Turkiya da Rasha Recep Tayyip Erdoğan viladimin Putin, sun sanya hanu kan yarjejeniya kan halin da arewacin siriya ke ciki.

Bayan wannan yarjejeniya, ministan harakokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya sanar da kawo karshen hare-haren da kasar Turkiya ke kaiwa kan kurdawan arewacin kasar ta Siriya.

Tun a ranar laraba 9 ga wannan wata na Oktoba da muke ciki ne kasar turkiya ta fara kai hare-haren kan yankunan kurdana na arewacin kasar Siriya wadanda take ganinsu a matsayin 'yan ta'adda.

A makon da ya gabata ce kasar Amurka ta cimma yarjejeniya da kasar Turkiya na dakatar da kai hare-haren na tsahon kwanaki biyar, wannan kuwa na zuwa ne bayan matsin lambar da shugaba Trump ya fuskanta a ciki da wajen kasar