Majiyoyin sojin kasar Syria sun sanar da cewa, rundunar sojin kasar na shirin karbar iko da birnin Qaqqah daga hannun dakarun Kurdawa.

Tashar Alalam ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da rundunar sojin kasar Syria ta fitar, ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin karbar birnin Raqqah da kewaye daga mayakan Kurdawa.

Wannan mataki na zuwa ne dai a daidai lokacin da Turkiya ta tura sojojinta a yankunan arewacin kasar ta Syria da sunan yaki da kungiyoyin Kurdawa da suke dauke da makamai, inda ya zuwa yanzu hare-haren na Turkiya sun yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama arewacin kasar ta Syria.

Mayakan Kurdawa sun janye daga yankuna da dama a rewacin kasar, inda sojojin Syria suke maye gurbinsu domin hana isowar sojojin Turkiya a cikin yankunan, wadabda suke kusa da iyaka da kasar ta Turkiya.
A nasa bangaren shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Erdogan ya ce babu gudu babu ja da baya a harin da yake kaddamarwa kan Kurdawan Syria, amma ya ce babu laifi idan sojojin gwamnatin Syria suka karbi iko da yankunan da Kurdawan suke iko da su.