Kungiyar tarayyar turai ta fitar da wani bayani wanda a cikinsa ta bayyana matsayarta kan cikar shekara da kisan gillar Khashoggi.

A cikin wani bayani da ta fitar mai magana da yawun kungiyar tarayyar turai ta bayyana cewa, bayan cikar shekara guda da kisan dan jaridar kasar Saudiyya Jamal Khashoggi, har yanzu akwai tambayoyi da suka rage wadanda gwamnatin Saudiyya ba ta amsa su ba kan wannan batu.

Bayanin ya ce har yanzu ba a ji bayani takamaimai kan wadanda suka aikata wannan ta’asa ba daga bangaren gwamnatin Sudiyya, da kuma wadanad suke da hannu cikin lamarin, wanda dole ne a yi hukunci na adalci kan wannan batu.

Tun a shekarar da ta gabata ce a rana irin ta yau, wasu manyan jami’an tsaron gwamnatin Saudiyya da suka hada har da masu tsaron lafiyar yarima mai jiran gado, suka yi tattaki musamman zuwa Turkiya, ida suka yi wa Jamal Khashogii kisan gilla, sannan kuma suka komakasar ta Saudiyya kafin asirinsu ya tonu.