Ayatullah Sayydi Ahmad Khatami: bayan idar da sallar juma’a da jagoranta anan Tehran ya bayyana cewa; Tattakin 40 na Imam Husain da ake yi ya sa duniya tana kara fahimtar sakon Imam Husain (a.s)
Ayatullah Sayydi Ahmad Khatami ya kara da cewa; Wadanda suke yin tattakin na araba’in, mutane ne da zukatansu suke cike da kaunar iyalan gidan manzon Allah, wacce a wannan lokacin ta zama mara tamka a duniya.

Limamin na Tehran ya kuma ce; Adadin masu yin tattakin na bana ya kai miliyan 20, da za su yi tafiyar kasa ta tsawon kilo mita 80, wanda an saba yi a gama lafiya cikin nutsuwa.

Limamin na Tehran ya yi ishara da dukkanin makirce-makircen da makiya su ka shriya domin gani ba a yi tattakin na bana ba, sai dai hakan ba zai sa mutane su fasa ba, koda kuwa wane cikas za a gindaya a gabasu, saboda shaukinsu da Imam Husain (a.s)